HANYOYI 10 DA ZAKA GANE KA CI KAI👇😂
1. Yayinda Kaine kake aiki cikin wahala da jurewa Rana Amma Budurwarka ce ke lashe Albashin. TO KA CI KAI 😂😂
2. Ka siyowa Budurwarka Suya Amma sai kake cin Albasa ba Naman ba. TO KA CI KAI 😂🤣
3. Ka siyo IPhone8 ga Budurwarka Amma wani saurayin na daban acan gefe yana browsing da ita. TO KA CI KAI 🤣😂
4. Kun shafe shekara 3 Kuna soyayya Amma aduk Lokacin da zata gabatar da kai ga kawayenta saita gabatar da kai a matsayin Aboki. TO KA CI KAI 🤣😂
5. Kace da ita Ina Sonki ta Mayar maka da Nima haka ka koma gefe kana ta washe Baki. TO KA CI KAI 🤣😂
6. Ka siya Mata katin waya na 500 Amma sai kace da ita idan ta saka katin tayi maka Flashing. TO KA CI KAI 😂🤣
7. Ka shafe tsawon Lokaci kana yi Mata Shopping Amma ko sau Daya Bata taba hada maka Abinci na Musamman kazo ka ci ba Koda da Azumi. TO KA CI KAI 😂🤣🤣
8. Ka siyo Mata sabbin Dinki Amma Bata taba saka su ba idan kazo zance sai zataje Unguwa. TO KA CI KAI 😂🤣
9. Kunje Restauranta ta lashe Abincin sama da 3500 Amma har kuka rabu batare data Furta maka kalmar I Love You ba. TO KA CI KAI 😂🤣
10. Ka karanta Post din Kuma ka nishadantu Amma ka tafi batare da kayi Comment ko Like ba. TO ARADU KA CI KAI 🤣😂🤣
