Kotu ta kwace gidajen da kwankwaso yagina

 


Kotu ta ƙwace gidajen da Kwankwaso ya gina da kuɗin ‘yan fansho a Kano


Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta bai wa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Nigeria (EFCC), umarnin ƙwace rukunin gidaje guda 324 waɗanda gwamnatin tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ta ɗebi kuɗin yan fansho ta gina su.


Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya dake Abuja shine yayi wannan hukuncin da safiyar yau Alhamis.

 


A cewar kotun gidajen an gina su ne ta hanyoyin haramun saboda an ɗebi kuɗin yan fansho ne aka gina.

 


Gidajen sun haɗa da: guda 168 na Sheikh Ja’afar Mahmud Adam waɗanda aka fi saninsu da rukunin gidajen Bandirawo da guda 122 na Sheikh Nasiru Kabara da akewa lakabi da Amana City sai kuma rukunin gidaje 38 a Khalifa Isyaka Rabi’u ko kuma Kwankwasiyya.


 

Kotun dai ta umarci EFCC da ta ƙwace gidajen halak malak


Tun farko hukumar EFCC ce ta gurfanar da gwamnatin Kano da kwamitin amintattu na yan fansho na jihar Kano tana zargin su da kwashe kuɗin yan fansho su gina gidaje

Post a Comment

Previous Post Next Post