TUNA BAYA: Shin Ko Za Ku Iya Tuna Wannan Matashiyar Budurwar Da Maza Suka Yi Rububin Zuwa Neman Aurenta A Kano?
Sunanta Zainab Abdulmalik, ita ce wadda sunanta ya karaɗe kafafen watsa labarai a shekarar 2015 inda taje har gidan Radio Freedom tace tana neman mijin aure, sannan za ta bada maƙudan kuɗaɗe tare da gida da mota ga duk wanda ya aure ta.
Samari da yawa sun rikice a jihar Kano suka yi ta zuwa gidan Radio ɗin tare da hotunansu ko wannan budurwar za ta yarda ta aure su.
Sai daga ƙarshe aka gano matar tana da taɓin hankali.
Daga Abdulrahim Yusuf Bulangu
Tags:
Nishadi
